Likitoci na shirin tsunduma yajin aiki nan da makonni 2


Kungiyar Likitocin masu neman kwarewa reshen birnin tarayya Abuja ARD ) ta yi wa Ministan Abuja Nyesom Wike, gargadin cewa membobinta za su fara garkame asibitoci tare da tsunduma yajin aiki cikin kwanaki 14 idan ba a biya bukatunsu ba.

Shugaban kungiyar, Dakta George Ebong, ne ya bayyana wannan gargadi a ranar Litinin yayin wani taron manema labarai a Asibitin Wuse, Abuja.

Yayin da ya yaba wa ministan kan ayyukan gine-gine da yake gudanarwa a Abuja, Ebong ya jaddada muhimmancin kula da walwalar likitoci da suke fuskantar barazanar mutuwa sakamakon tsananin rayuwa

A cewarsa, ya kamata ministan ya mai da hankali kan ci gaban dan Adam kamar yadda yake yi a bangaren gine-gine.

Ya bayyana cewa ministan FCT na da kwanaki 14 don daukar mataki kan bukatun don kauce wa abin da ya kira matakin rufe asibitocin a birnin tarayya da kungiyar zata dauka.

“Muna fara godiya ga ministan bisa ayyukan gine-ginen da ya gudanar a FCT tun bayan hawansa.

“Muna so ya san cewa likitoci sun zama kamar wadanda aka manta da su. Yayin da yake gyara ayyukan gine-ginen da aka manta, mu kuma muna matsayin ‘wani bangare na al’umma da aka manta. Muna da tabbacin cewa ministan zai iya magance wannan kalubale.

“Muna so ministan ya biya albashin watanni shida da membobinmu ke bi, tun 2023.

“Haka nan, a gaggauta biyan kudaden horar da likitoci na 2024.

“Bugu da kari, muna so ministan ya duba dokar sanya wa’adi zuwa shekaru biyu maimakon shida.

“Sauran bukatun sun hada da: Ministan ya tilasta aiwatar da tsarin tsallake mukamai tare da bayar da wasikun tabbatarwa ga membobinmu da aka dauka aiki a 2023; a gaggauta biyan kudin kayan aiki na 2024; a biya tsoffin kudaden alawus na watanni 13 na hadari; kuma hukuma ta hanzarta daukar ma’aikatan lafiya don cike gibin karancin ma’aikata a asibitocin babban birnin tarayya.





Source link

Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *