Tinubu ya fara kuskure tun ranar rantsarwa – Tinubu


Wani jigo a jam’iyyar Labour Party (LP), Kenneth Okonkwo, ya caccaki Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, yana cewa ya fara aikata kuskure tun ranar da aka rantsar da shi.

Okonkwo ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a tashar Channels Telebijin, inda ya yi nazari kan tattaunawar farko da Tinubu ya yi da manema labarai.

Tsohon ɗan wasan kwaikwayon na Nollywood ya bayyana cewa, “Tun bayan wata 19, Shugaban Ƙasa bai iya bayyana wa ‘yan Najeriya abin da yake yi ba.”

“Dimokraɗiyya ba wai kawai magana da mutane ba ce, ya zama wajibi shugabanni su fuskanci tambayoyi daga wajen mutane.

Okonkwo ya kuma caccaki Tinubu saboda dora laifi dayayi kan masu shirya rabon tallafi da ke haifar da turereniya, wanda hakan ya yi sanadin mutuwar mutane da dama a Najeriya.

“Shugaban Ƙasa ya dora dukkan alhakin kan masu shirya wannan rabon tallafi, wadanda suka so taimaka wa mutanen da ke cikin yunwa. Bari in fada muku, wannan turereniyar da turmutsutsin ta faru a Gabas, Yamma da Arewa. Wannan yana nuna cewa yanzu yunwa ta zama gama-gari a Najeriya, kuma abubuwa sun yi tsauri,” in ji shi.





Source link

Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *