An kama jigon NNPP a jihar Borno


Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Borno ta kama wani jigo a jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Atom Magira, bisa zargin sa da sukar Gwamna Babagana Zulum.

Mataimakin Magira, Mohammed Yahaya, ya bayyana cewa an dauke Magira ne a daren Lahadi ta hannun jami’an hukumar.

Magira, wanda a baya ya yi takarar gwamna a jam’iyyar (APC) a zaben shekarar 2019, yana daga cikin manyan yan adawa a jihar. Ya kasance mai sukar wasu daga cikin manufofin Gwamna Babagana Zulum.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce an tsare Magira ne saboda wani allon talla da magoya bayansa suka sanya mai dauke da “YES TO MERGER”, wanda ke kira da hadewar dukkan jam’iyyun siyasa a jihar.

“Har yanzu Magira na tsare har zuwa safiyar Litinin, amma ba a san ko za a tura shi kotu ba,” in ji wani mai ruwa da tsaki wanda ya nemi a boye sunansa.





Source link

Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *