INTERPOL ta Fitar da sunayen ’Yan Najeriya 14 da Ake nema ruwa a Jallo Saboda laifuka Daban-daban
Hukumar ‘yan sandan kasa da kasa (INTERPOL) ta wallafa sunayen ’yan Najeriya 14 da ake nema saboda aikata laifuka kamar safarar mutane, miyagun kwayoyi, sata, damfara, da zamba.
A cewar sanarwar da aka wallafa a shafin yanar gizon INTERPOL, wadannan mutanen suna fuskantar tuhuma a kasashe daban-daban saboda aikata wadannan laifukan.
Sunayen wadanda ake nema sun hada da:
Felix Omoregie: Ana zarginsa a Belgium da jagorantar wata kungiya ta laifi da ke shigar da yara karuwanci.
Jessica Edosomwan: Ana nemanta a Faransa kan safarar mutane da aikata laifuka a karkashin kungiyoyin asiri.
Jude Uzoma, Uche Egbue, Chinedu Ezeunara, Benedict Okoro: Ana tuhumar su da safarar miyagun kwayoyi a kasashe daban-daban kamar Venezuela, Uruguay, da Argentina.
Ikechukwu Obidiozor, Alachi Stanley, da Akachi Vitus: Suna fuskantar tuhuma a Angola kan satar mutane, fashi da makami, da mallakar makamai ta haramtacciyar hanya
Timloh Nkem: Ana nemansa a Canada saboda zargin fyade da rashin kin bin sharadin belinsa.
Bouhari Salif: Ana zarginsa a China da safarar miyagun kwayoyi.
Austine Costa da Okromi Festus: India tana tuhumar su da zamba da hada-hadar takardun bogi.
INTERPOL ta bayyana cewa sanarwar na neman taimakon jama’a wajen gano wadanda ake zargi,