Majalisar dokokin Kano ta mika sakon Kirsimeti ga mazauna jihar


Majalisar dokokin Kano ta bukaci mabiya addinin kirista da suyi amfani da lokutan bukukuwan kirsimeti da sabuwar shekara wajen mayar da hankali domin yin addu’o’in samun saukin matsin rayuwar da ake ciki a kasar nan.

Shugaban majalisar Jibril Isma’il Falgore ne ya bayyana hakan ta cikin sakon taya murna daya aike ga mabiya addinin kiristar dake kasar nan.

Falgore, ta bakin babban sakataren yada labaran Majalisar dokokin ta Kano, Kamaluddeen Sani Shawai ya ce sakon majalisar wata alama ce ta kyakyyawar mu’amalar dake tsakanin mabiya addinai daban-daban a kasar nan.

Falgore ya kuma bukaci mabiya addinin na kirista dake jihar nan da su ci gaba da ba wa gwamnati da Majalisar dokokin ta Kano cikakken hadin kai da goyon bayan daya dace domin ciyar da Kano gaba da kowace fuska.

Kakakin majalisar Falgore ya kara jaddada kudurin su na cigaba da marawa gwamnatin jiha baya akan dukkan manufofinta wadanda suke nufin samar da kyakkawan muhallin rayuwa ga kowa ba tare da banbancin addini ko kabila ba.





Source link

Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *