EFCC ta kama Akanta janar ta jihar Delta bisa zargin badakalar sama da N1trn


Jami’an Hukumar EFCC sun kama Akanta Janar na Jihar Delta, Misis Joy Enwa, a cikin binciken da ake yi kan zargin karkatar da Naira tiriliyan 1.3 na kudaden jihar da ake danganta wa da tsohon Gwamnan Jihar, Ifeanyi Okowa.

Hukumar EFCC tana bincike kan zargin karkatar da kudaden kaso 13 cikin 100 da aka ware wa jihohi masu arzikin mai, wanda ake zargin Okowa ya sace yayin da yake gwamna.

An kama tsohon gwamnan a watan Nuwamba na bana tare da tsare shi a ofishin EFCC da ke Port Harcourt, saboda rawar da ake zargin ya taka wajen karkatar da kudaden.

Ana zargin ya yi amfani da mukaminsa na gwamna wajen mallakar kadarori da suka kai kimanin Naira tiriliyan 1.3, ciki har da hannun jari a kamfanin UTM Floating Liquefied Natural Gas Company, tare da zuba jari a bangaren albarkatun man fetur.

Hukumar tana ci gaba da gudanar da bincike kan zargin karkatar da kudaden, inda aka kama wani tsohon darakta na kudi da gudanarwa, Ekeruche, da daraktan gudanarwa na gidan gwamnati, domin yi musu tambayoyi.





Source link

Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *