Wike da ‘ya’yansa sun ziyarci Tinubu a Legas [Hotuna]


Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, tare da ‘ya’yansa, Jordan da Joachin, sun kai ziyara ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a gidansa da ke titin Bourdillon, Ikoyi, Lagos, a ranar Kirsimeti.

Mataimakin Musamman na Wike kan Hulɗar Jama’a da Sabbin Kafofin Sadarwa, Lere Olayinka, ne ya bayyana hakan a wata wallafa da ya yi a shafinsa na X a safiyar Juma’a.

A yayin ziyarar, Shugaba Tinubu ya tarbi iyalin Wike cikin farin ciki tare da yabawa kokarin ministan wajen inganta birnin tarayya, Abuja.

Tinubu ya jinjina wa Wike bisa jajircewarsa kan magance manyan matsaloli a Abuja, ciki har da inganta tsarin kula da filaye da tabbatar da bin dokoki.

A cewarsa: “Wike mutum ne mai aiki tukuru wanda ya nuna jajircewa wajen magance matsalolin da ke addabar babban birninmu. Muna godiya ga irin gudunmawar da yake bayarwa don tabbatar da ci gaba da inganta Abuja.”

Ministan ya gode wa Shugaba Tinubu bisa karimci da tarba mai kyau, yana mai cewa zai ci gaba da aiki tukuru don ciyar da babbar birnin tarayya gaba.





Source link

Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *