2024: Mutum 222 sun mutu a hadura a Oyo – FRSC


Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) ta bayyana cewa, mutum 222 ne suka rasu a sakamakon haduran mota akan hanya a Jihar Oyo a shekarar 2024.

Hukumar ta bayyana haka ne cikin kididdigar karshen shekara, wadda Misis Rosemary Alo, kwamandan hukumar ta jihar Oyo, ta sanya hannu a kai.

Alo ta ce wannan adadin yana nuni da raguwar mace-macen rayuka idan aka kwatanta da mutanen da suka rasa rayukansu a shekarar 2023, wadda adadinsu ya kai 270.

A cewarta, adadin ya samo asali ne daga hadura 304 da aka samu a shekarar 2024, yayin da aka samu hadura 495 a shekarar 2023.

Kwamandan sashen ta jaddada cewa, kididdigar ta nuna cewa mutum 779 ne suka samu raunuka a haduran kan hanya a shekarar 2024, idan aka kwatanta da 1,321 da aka samu a shekarar 2023.

“Mutum 1,795 ne suka shiga haduran hanya a shekarar 2024, yayin da 2,935 suka shiga hadura a shekarar 2023,” in ji ta.

Ta kara da cewa, adadin motoci da suka samu hadura ya ragu zuwa 412 a shekarar 2024 daga 794 da aka samu a shekarar 2023.

Kwamandar ta danganta raguwar haduran kan hanya a shekarar 2024 da shirye-shiryen wayar da kan jama’a da masu ruwa da tsaki ke aiwatar da kuma tsauraran matakan aiwatar da dokokin hukumar a shekarar 2024.

Alo ta kara da cewa, hukumar ta gudanar da ayyukan wayar da kan jama’a a shekarar 2024, inda ta yi kira ga fasinjoji suyi amfani da hakkinsu wajen magana idan direba na tuki cikin rashin kula.

Ta shawarci direbobi da fasinjoji su dauki alhakin lafiyarsu a hanya tare domin gujewa asarar rayuka da dukiyoyi.





Source link

Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *