Aboki mai tausayi – Tinubu yayi jimamin mutuwar Carter


Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya nuna alhininsa kan rasuwar tsohon shugaban kasar Amurka, Jimmy Carter.

Daily Post ta ruwaito cewa Carter, wanda yayi mulki a matsayin shugaban Amurka daga 1977 zuwa 1981, ya rasu yana da shekaru 100.

A wata sanarwa daga Fadar Shugaban Kasa a ranar Litinin, Tinubu ya mika ta’aziyyarsa ga gwamnatin Amurka da al’ummarta.

“Shugaba Carter ya nuna mana yadda ake kasancewa masu tasiri da amfani ga al’umma bayan barin kujerar shugabancin Amurka,” in ji Shugaba Tinubu.

Ya kara da cewa, “Ya mayar da hankali kan kalubalen da kasashen da ke tasowa ke fuskanta, daga yaki da cututtuka zuwa shiga tsakani wajen sasanta rikice-rikice da kare darajar dimokuradiyya. Ya kasance misalin mutunci, da girmamawa.”

Tinubu ya bayyana Jimmy Carter, shugaban kasar Amurka na 39, a matsayin “fitila mai haskakawa hidiman bil’adama,” yana mai cewa ya zama abin koyi ga shugabanni a duk duniya kan yadda zasuyi tasiri mai ma’ana bayan mulki.





Source link

Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *