An samar da kwamitin tsaftace Kasuwar Kantin Kwari


Hukumar gudanarwar kasuwar Kantin Kwari, ta kaddamar da kwamitin tsaftace kasuwar da nufin magance matsalolin dake addabar masu saye da sayarwa.

Shugaban hukumar Hamisu sa’adu Dogon Nama ne ya jagoranci kaddamarwar a wani rangadi da suka gudanar da nufin fadakar da ‘yan kasuwar game da aikace-aikacen kwamitin da aka samar.

Dogon Nama ya ce kwamiti zai gudanar da aikace-aikace a kasuwar a dukkan bangarorin hada-hadar kasuwanci, da samar da ingantaccen tsaro da dai sauransu.

A nasa jawabin shugaban kwamitin tsaftace kasuwar ta kantin kwari Abdullahi Abubakar Rijiya Hudu ya ce zasu yi aiki tukuru wajen kawo sauye-sauyen da zasu ciyar da kasuwar gaba da suka hada da hana lodi ga direbobi wanda ya saba ka’ida da kuma kawar da cinkoso.

Daga cikin ‘yan kwamitin da zasu gudanar da tsaftace kasuwar sun hada da jami’an tsaro na ‘yan sanda, imagration, Karota da civil defence da Hisba da dai sauran ‘yan kasuwar ta Kantin kwari.





Source link

Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *