ASUU ta na shirin fara yajin aiki a watan Janairu, 2025


Kungiyar malaman jami’oi ta kasa ASUU ta ce dalilin da ya sa bata tsunduma yajin aikin da ta ke barazaranar yi ba tsawon watanni shine domin kara ba gwamnatin dama ta magance matsalolin kungiyar nan da farkon shekarar 2025.

Shugaban kungiyar na kasa Professor Emmanuel Osodeke ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da manema labarai a karshen mako,inda ya ce za su cigaba da ba gwamnati dama domin ganin irin matakin da zata dauka.

Farfesa Osodeke ya bayyana rashin jin dadi a kan yadda gwamnati ta ki kula da kalubalen da su ka gabatar mata.

Ya ce daga shekara mai zuwa, za su sake zama domin daukar mataki na gaba.





Source link

Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *