EFCC ta gargadi ‘yan Najeriya kan rashawa a 2025


Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta gargadi ‘yan Najeriya da su guji aikata ayyukan rashawa a shekarar 2025, tare da himmantuwa wajen yaki da cin hanci domin ci gaban kasa.

Shugaban hukumar, Ola Olukoyede, ya yi wannan gargadin a ranar Talata, inda ya bayyana cewa nasarar kasar nan tana tattare da kokarin kowa da kowa wajen dakile laifukan cin hanci da rashawa.

A cikin sakon sabuwar shekara da ya aika wa ‘yan kasa, Olukoyede ya jaddada cewa gujewa rashawa shine ginshikin da zai inganta rayuwar ‘yan Najeriya da bunkasa tattalin arzikin kasa.

Ya ce: “Za mu iya cimma duk wani cigaba da muke so a kasar nan ta hanyar goyon baya ga ayyukan yaki da rashawa. Sabuwar shekara ta ba mu damar sake jajircewa kan dabi’un gaskiya, amana da rikon amana.”

Shugaban hukumar ya kara da cewa: “Ci gaban tattalin arziki da ingantuwar rayuwar mu zai dogara ne da jajircewar mu wajen gaskiya da rikon gaskiya.”

Olukoyede ya tabbatarwa da ‘yan Najeriya cewa EFCC za ta zarce nasarorin da ta samu a shekarar 2024, tare da alkawarin cewa jami’an hukumar za su ci gaba da ba da gagarumin gudunmuwa a fagen yaki da rashawa.





Source link

Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *