Gwamna Dapo Abiodun ya nada sabon Shugaban Ma’aikatan gidan gwamnati


Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya nada Oluwatoyin Taiwo a matsayin sabon Shugaban Ma’aikata na ofishinsa. Gwamnan ya mika masa takardar nadin ne a ranar Laraba, 18 ga Disamba, 2024.

A wata sanarwa da mai bai wa gwamnan shawara kan kafafen watsa labarai Kayode Akinmade ya fitar, an bayyana cewa nadin ya fara aiki nan take.

Kafin wannan mukamin, Taiwo yana rike da matsayin Mataimakin Shugaban Ma’aikata (DCOS) a ofishin gwamnan. Haka zalika, ya taba rike mukamin Kwamishinan Al’adu da Yawon Bude Ido a wa’adin mulki na farko na Gwamna Abiodun.

Oluwatoyin Taiwo ya yi karatun digiri na farko a fannin kididdiga a jami’ar Obafemi Awolowo, Ile-Ife, inda ya samu digirin B.Sc. daga nan ya ci gaba da karatu har zuwa matakin digirin digirgir(PhD).





Source link

Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *