Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sa hannu a kan dokar kasafin kudin shekarar 2025, wanda ya tasamma sama da Naira biliyan 719.
Gwamna Yusuf ya amince da sanya hannu a kan kasafin ne bayan majalisar dokokin Kano ta yi kari akan dokar kasafin daga sama da Naira biliyan 549 zuwa Naira biliyan 719.
Karin kasafin kudin ya biyo bayan korafe-korafen da jama’a da kungiyoyi suka yi na bukatar hakan , lokacin sauraren ra’ayin jama’a da aka shirya a majalisar dokokin Kano a ranar 12 ga watan Nuwanba na 2024.
Gwamnan Kano ya gabatarwa majalisar dokokin Kano kasafin ne a ranar 8 ga watan Nuwanba na shekarar 2024, daga nan kuma hukumomi da ma’aikatun gwamnati suka kare abin da aka tura musu.
Bangaren ilimi shi ne yafi jan kaso mafi tsoka da kashi 31 cikin 100 na kasafin .
Yayin da yake sa hannun a gaban yan majalisar dokokin Kano karkashin jagorancin Shugaban majalisar, Jibiril Isma’ila Falgore, gwamna Yusuf ya tabbatar da cewa a ranar 1 ga watan Janairun sabuwar shekarar 2025 kasafin zai fara aiki
A jawabinsa, Shugaban majalisar dokokin Kano, Hon Falgore yayi fatan cewa kasafin zai taimaki mutanen kano a shekarar ta 2025.
Gwamna Yusuf ya nemi dukkanin ma’aikatun da suke da alhakin aiwatar da kasafin da aka tura musu da su yi kyakkyawan amfani da shi yadda ya kamata.
Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da cewa kasafin zai maida hankali wajen inganta tattalin arzikin jama’ar Kano da samar da aikin yi ga matasa da walwalar jama’a da yaki da talauci da kuma yunwa.
Ya kuma godewa al’umar Kano,da sauran kungiyoyin fararen hula da suka taimaka kasafin kudi ya tabbata.
Gwamna ya godewa manema labarai abisa gudunmowar da suke bayarwa.