Gwamnati za ta gyara duk manyan tituna kafin Kirsimeti – Umahi


Ministan ayyuka, Dave Umahi ya ce gwamnatin tarayya na aiki don tabbatar da cewa dukkanin manyan hanyoyin tarayya za su biyu iya kafin Kirsimeti.

Umahi ya yi wannan bayani ne a Akure, babban birnin jihar Ondo, a ranar Alhamis yayin taron da gwamnati da ma’aikatar ayyuka ta shirya.

Ministan ya ce gwamnatin ta gaji ayyukan gina hanyoyi sama da 2,000 da ba a kammala ba, wadanda suka kai biliyoyin Naira, yana mai cewa gwamnati ta soke kwangiloli 10 na kamfanonin da ba su bi ka’ida ba.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya da ta jihar Ondo suna da niyyar dawo da al’ummar Aiyetoro da ke fuskantar barazanar mamayar uwan teku.

“Mun soke kwangiloli fiye da 10 na manyan kamfanoni, kuma muna da niyyar soke wasu karin kwangiloli, ba za ku iya nuna mana abin da za mu yi ba, za mu gaya muku abin da muke so,” in ji Umahi.

“Mun umurci dukkan masu kula da hanyoyin tarayya su ba mu cikakken bayani game da hanyoyin da ke cikin yankin su, ko an ba da kwangila ko a’a, domin kafin Kirsimeti, dukkanin manyan hanyoyin tarayya za su zama a gyare.”

Ministan ya kuma bayyana cewa layin kilomita 63 na hanya ta gabar tekun Calabar-Lagos a jihar Ondo zai kasance an kaddamar da shi a watan Disamba.





Source link

Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *