Gwamnatin tarayya ta ja kunnen yan adawa a kan siyasantar da mutuwa a turereniya


Ministan labarai Mohammed Idris, ya yi kira ga ‘yan siyasa da su daina danganta hadarin turereniya da aka samu yayin rabon abinci a jihohin Oyo, Anambra da Abuja da sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta kawo.z,c

A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Rabiu Ibrahim, ya sanya wa hannu, Ministan ya bayyana juyayin sa ga iyalan wadanda suka rasa rayukan su a cikin munanan abubuwan da suka lakume rayukan sama da mutane 70, ciki har da yara kusan 40.

Ya ce wadannan al’amuran sun nuna muhimmancin tabbatar da isasshen tsarin kula da jama’a yayin gudanar da irin wannan rabon taimako, musamman a lokutan bukukuwa.

Idris ya yaba wa masu shirya irin wadannan ayyuka na alheri domin rage radadin wahala ga marasa karfi, amma ya gargadi duk wanda zai gudanar da irin wannan aiki da su yi aiki tare da rundunar ‘yan sanda bisa umarnin Sufeta Janar na ‘Yan sanda, Kayode Egbetokun, da kuma Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), domin inganta tsaro da hana aukuwar irin wannan bala’i.

Ya yi kira ga ‘yan siyasa da su daina amfani da wadannan abubuwan domin siyasa, yana mai jaddada cewa ba su da wata alaka da manufofin tattalin arzikin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ministan ya kara da cewa, ya kamata a fahimci cewa irin wadannan abubuwa masu ban takaici sun taba faruwa a baya kafin wannan gwamnati, don haka duk wani kokarin danganta su da sauye-sauyen gwamnati ba gaskiya ba ne.





Source link

Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *