Gwamnonin Ekiti da Nasarawa Sun Rattaba Hannu Kan Kasafin Kudin Shekarar 2025


Gwamnan Jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, da takwaransa na Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, sun rattaba hannu kan kasafin kudin shekarar 2025 na jihohinsu a ranar Litinin.

Kasafin kudin Jihar Ekiti ya kai Naira biliyan 375. A jawabinsa bayan rattaba hannu a ofishin gwamna da ke Ado-Ekiti, Oyebanji ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su goyi bayan kudirin gyaran haraji da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar.

Ya ce hakan zai amfani kasa baki daya. Ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa za ta yi kokarin cimma burin samun kudaden shiga domin aiwatar da shirye-shiryen ci gaba da suka tsara.

A Jihar Nasarawa kuwa, Gwamna Abdullahi Sule ya rattaba hannu kan kasafin kudin shekarar 2025 da ya kai Naira biliyan 384.3, wanda ya haura fiye da Naira biliyan 2 bisa kiyasin da ya gabatar wa majalisar jiha tun farko.

Yayin da yake rattaba hannu a gidan gwamnati da ke Lafia, Gwamna Sule ya yaba wa kakakin majalisar Jiha da sauran ‘yan majalisa saboda jajircewarsu wajen gaggauta amincewa da kasafin kudin.





Source link

Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *