Janar Musa yayi alkawarin kama Bello Turji


Shugaban Rundunar Sojojin Najeriya, Janar Christopher Musa, ya yi alkawarin ganin an kamo shugaban ‘yan bindiga, Bello Turji.

Musa ya ce lokaci kadan ne kafin a kama Turji saboda wasu daga cikin kwamandan sa sun rasa rayukansu, yayin da suka kama wasu daga cikin manyan abokansa.

Ya bayyana wannan ne a cikin shirin Channels Television na “2024 Year-In-Review” a ranar Talata.

A cewar sa: “Sabon bayanin shine tun da ya san cewa muna bibiyar sa, yanzu yana gudanar da ayyukansa a kasa, kuma muna gudanar da ayyukan soji.

“Abin da muka mayar da hankali a kai kwanan nan shine mu na kama duk wanda ke kusa da shi; dukkan wanda suke ba shi goyon baya ta kowace hanya, mun kama su, mun kashe kwamandansa. Lokaci kadan ne kafin mu kama shi.”

Shugaban Rundunar Sojojin ya kuma bayyana cewa sama da ‘yan ta’adda 120,000 sun tuba a Arewa maso Gabas.

Ya jaddada cewa wasu daga cikinsu an tilasta musu shiga aikin ta’addanci.





Source link

Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *