Jigawa: Amarya ta zuba guba a abincin biki


Wani biki a Jihar Jigawa ya rikide zuwa tashin hankali bayan da aka zargi amarya da guba abincin da aka yi hidima da shi a wajen liyafar bikin.

An ce lamarin ya jefa ango cikin mawuyacin hali tare da jawo mutuwar daya daga cikin bakin bikin.

Abin ya faru ne a karamar hukumar Jahun ta jihar Jigawa.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar, SP Shi’isu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an fara bincike.

“Muna da rahoton cewa amarya ta zuba guba a abincin biki…Yan sanda sun kama mutane biyu dangane da zargin wannan lamari na zuba guba a cikin abincin.”

Ya bayyana cewa wadanda ake zargin biyu su ne amarya da wata mace daya, yana mai cewa suna hannun ‘yan sanda kuma ana musu tambayoyi a sashen binciken manyan laifuka na rundunar.

Kakakin ‘yan sandan ya kara da cewa, “Za mu yi duk abin da ya dace don tabbatar da cewa an yiadalci.”

A cewar kakakin, duk bakin bikin da suka ci abincin da aka zuba guba samu sauki, illa mutum daya da ya koma ga Allah.





Source link

Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *