Jihar Bayelsa ta baiwa ma’aikata hutun mako guda


Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa ya bada hutun mako guda ga ma’aikatan jihar a matsayin wani bangare na bikin Kirsimeti.

A cewar sanarwar da Kwamishiniyar labarai ta jihar Hajiya Ebiuwou Koku-Obiyai, ta fitar, hutun zai fara daga ranar 24 ga Disamba, 2024, zuwa ranar 30 ga Disamba, 2024.

Duk da haka, ma’aikatan da ke gudanar da ayyukan gaggawa ba su cikin waɗanda wannan hutun ya shafa; za su ci gaba da aikin su a cikin wannan lokacin.

Gwamna Diri ya gode wa al’ummar jihar Bayelsa bisa goyon bayan da suke bayarwa tare da yin fatan alheri na bikin Kirsimeti mai cike da annashuwa da Sabuwar Shekara mai albarka.





Source link

Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *