Jihohin Yobe, Sakkwato da Bauchi sun samar da hukumar Hisba


Hukumar Hisba ta Jihar Kano bayyana cewa samar da hukumomin Hisba a jihohin Arewa zai taimaka wajen magance matsalar aikata bada a yankin.

Kwamandan na Hisba a Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne ya bayyana hakan bayan kammala Ziyara zuwa jihohin Yobe, Bauchi, da Sokoto, inda ya bayyana cewa jihohin suna kokarin samar da hukumomin Hisba kamar yadda Kano ta samar da ta a shekarar 2003 a zamanin gwamnan Kano na lokacin, Rabiu Musa Kwankwaso.

A shekarar 2005, a lokacin gwamna Malam Ibrahim Shekarau, aka mayar da ayyukan hukumar doka a Majalisar Dokokin Kano.

Sheikh Daurawa ya shaida cewa jihohin Yobe, Bauchi, da Sokoto sun yarda da samar da hukumar Hisba domin magance matsalolin zamantakewar jama’a da kuma ayyukan da ke saba wa al’adun al’umma.

Jihohin Yobe, Sokoto, da Bauchi sun nemi shawarwarin kwamandan hukumar Hisba ta Kano kafin su kaddamar da hukumomin Hisba a jihohinsu.

A yayin da yake karin haske bayan kammala ziyarar zuwa wadannan jihohi, Sheikh Daurawa ya ce hukumomin Hisba za su hada karfi domin magance matsalolin yawon almajirai da mata masu zaman kansu.





Source link

Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *