Alhaji Sagir Sani Rano, fitaccen dan kasuwa kuma mai taimakon jama’a daga Karamar Hukumar Rano, ya jinjinawa Rt. Hon. Kabiru Alhassan Rurum (Turakin Rano) kan gagarumin ci gaban da ya samar a mazabar Rano, Kibiya da Bunkure.
A wata sakon taya murnar zagayowar ranar haihuwar Rurum ta 55 da ya aikawa manema labarai a Kano, Sagir Rano ya bayyana Hon. Rurum a matsayin jagora mai kishin jama’a da kuma mai kaunar al’umma.
Yace: “A yayin da muke murnar cikar Rt. Hon. Kabiru Alhassan Rurum shekaru 55, ina mai taya shi murna tare da jinjinawa wannan babban jagora da ya sadaukar da rayuwarsa wajen bunkasa al’ummar Rano, Kibiya da Bunkure. Ayyukansa sun zama wani misali na shugabanci na gari.”
Alhaji Sagir ya yabawa Hon. Rurum kan ayyukan ci gaba da suka hada da gina tituna daga Rano zuwa Madachi, daga Zinyau zuwa Kasuwar Dila, da daga Kibiya zuwa Nariya a Karamar Hukumar Kibiya.
Haka zalika, ya jinjina masa kan samar da makarantu, cibiyoyin kiwon lafiya, da kuma kafa makarantar mata ta sojojin sama a Rano.
Yace: “Tarihin rayuwarsa na cike da gwagwarmaya da sadaukarwa don bunkasa walwalar al’umma. Daga gina tituna, makarantu, da cibiyoyin kiwon lafiya, zuwa bayar da tallafin karatu da shirye-shiryen bunkasa matasa da mata, Rurum ya nuna cewa yana tare da jama’arsa.”
Sagir Rano ya kuma yaba wa Hon. Rurum kan bayar da tallafin karatu ga daliban da basu da karfi da shirye-shiryen tallafi na musamman da ya gudanar don bunkasa matasa da mata.
Ya ce: “Shirye-shiryensa na tallafawa mata da matasa sun tabbatar da cewa yana kaunar cigaban jama’arsa. Mun gode masa kan abubuwan alkhairi da ya kawo wa mazabarsa.”
Alhaji Sagir ya kuma yi amfani da damar wajen yi wa Hon. Rurum fatan alheri da nasarori a rayuwarsa.
Yace: “A wannan rana ta musamman, muna fatan Allah ya kara masa lafiya, hikima, da kwarin gwiwa don ci gaba da yi wa jama’a hidima.”