- Kungiyar Amnesty International ta yi kira da a gudanar da bincike kan kashe mutane 10 a wani harin sama da sojojin Najeriya suka kai a ranar Kirsimeti a karamar hukumar Silame da ke jihar Sokoto.
Daraktan kungiyar a Najeriya, Isa Sanusi, ya ce, “Kai hare-haren sama ba wata hanya ce da ta dace ta gudanar da aikin tabbatar da doka ba, ko da a wane mataki ne.
“Irin wannan amfani da karfin makamai da gangan ba bisa ka’ida ba, abin takaici ne kuma ya bayyana yadda sojojin Najeriya ke raina rayukan wadanda ya kamata su kare.”
Mr. Sanusi ya ce amfani da karfi da gangan da sojojin Najeriya suka yi a al’ummomin da ke Sokoto ya halaka gaba ɗaya wani iyali a harin sama.”
“Gaba ɗaya iyalai sun mutu a cikin gidajensu. Wasu mazauna ƙauyen sun ƙone kurmus a wata gobara da hare-haren sama suka haddasa.
“Dokokin jinƙai na duniya sun tanadi cewa dole ne a dauki duk matakan da suka dace don rage illa ga fararen hula.”
“Hukumomin Najeriya su gaggauta gudanar da bincike kan yadda aka yanke shawara da yadda aka aiwatar da hare-haren sama da suka haifar da mutuwar fararen hula a Jihar Sokoto,” in ji Amnesty International.