Kungiyar kwallon kafa ta Enyimba ta kori kocinta


Kungiyar Kwallon Kafa ta Enyimba ta sanar raba gari da kocinta Yemi Olarenwaju nan take.

A wata gajeriyar sanarwa da kungiyar ta wallafa a shafinta na X, ta bayyana godiya ga Koci Olarenwaju bisa gudunmawarsa, tare da yi masa fatan alheri a gaba.

Sanarwar ta ce:

“Kungiyar Enyimba na sanar da cewa ta rabu da babban kocinta, Yemi Olarenwaju.

“Kungiyar tana godiya ga Koci Olarenwaju bisa gudunmawarsa, kuma tana masa fatan alheri a gaba.”

Koci Olarenwaju ya fara aiki da kungiyar a watan Satumbar 2022, lokacin da aka nada shi a matsayin mataimakin kocin Finidi George.

A lokacin da suke aiki tare, sun jagoranci Enyimba zuwa lashe kambun gasar firimiya ta Najeriya karo na tara, wanda shi ne mafi yawa a tarihin gasar.

Bayan murabus din Finidi George a watan Mayu 2024, Koci Olarenwaju ya karbi ragamar kungiyar a matsayin rikon kwarya, har zuwa karshen kakar wasa. Daga baya aka tabbatar da shi a matsayin babban koci a watan Agusta 2024.





Source link

Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *