Kungiyar Likitocin masu neman kwarewa a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Kimiyya ta Jihar Ondo sun fara yajin aiki na sai baba ta gani saboda rashin biyan albashi da kuma mummunan yanayin aiki.
A ranar Litinin, likitocin sun gudanar da zanga-zangar lumana dauke da kwalaye dauke da rubuce-rubuce daban-daban a cikin asibitin UNIMEDTH domin nuna damuwarsu.
Daga cikin manyan korafa korafansu, sun hada da matsalolin da ake da su kan biyan albashi da aiwatar da sabon tsarin mafi ƙarancin albashi.
Sauran bukatun sun hada da biyan bashin tallafin haɗari, samar da wuraren zama ga likitocin dake cikin asibitin, da daukar ma’aikata domin ƙara ƙarfin aiki a sassan da suka shafi likitanci, da sauransu.
A cikin wata sanarwa da ta bayyana farawar yajin aikin a ranar Talata, Shugaban kungiyar a jihar, Olaogbe Kehinde, ya ce likitocin sun gaji kuma ba za su iya ci gaba da aiki ba sakamakon rashin biyan bashin su da sauran hakkokinsu.