Ma’aikatar lafiya ta Kano ta kafa kwamitin kula da jini


Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ta kaddamar da Kwamitin Fasaha kan Kula da Jini domin magance matsaloli da inganta ingancin jinin da ake amfani da shi a asibitocin jihar.

A wata sanarwa da mai yadda labarai na ma’aikatar, Ibrahim Abdullahi, ya fitar a ranar Alhamis, 2 ga Janairu, 2025, kwamishinan lafiya na jihar, Dr. Abubakar Labaran Yusuf, ya jagoranci bikin kaddamarwar.

Da yake jawabi yayin kaddamarwar, Dr. Labaran ya bayyana cewa kwamitin an kafa shi ne domin tabbatar da tsaron jinin da ake amfani da shi a jihar.

“Dalilin kafa wannan kwamiti shi ne don tabbatar da tsaro da ingancin jini a jihar Kano.

“Yin aiki a irin wannan kwamitin tarihi ne da zai shiga kundin tarihi na Kano,” in ji Dr. Labaran.

Ya bayyana tabbacin cewa membobin kwamitin za su gudanar da aikin yadda ya kamata.

Dr. Labaran ya godewa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa goyon bayansa ga shirye-shiryen inganta harkar lafiya a jihar, wanda ya ce shi ne ya ba da dama ga kafa kwamitin.

Kwamitin wanda Dr. Musbahu Rabi’u, Daraktan Sashen Kula da Lafiya na Hukumar Gudanar da Asibitoci, yake jagoranta, zai bayar da shawara ta fuskar fasaha, samar da dokoki da tsare-tsare kan amfani da jini, tare da tabbatar da hadin gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki a fannin lafiya.

Da yake magana a madadin mambobin kwamitin, Dr. Rabi’u ya tabbatar da cewa za su yi iya kokarinsu wajen cika nauyin da aka dora musu.

“Za mu yi duk kokarin mu don tabbatar da an gudanar da wannan aiki yadda ya kamata,” in ji shi.

Kwamitin ya kunshi wakilai daga manyan cibiyoyin lafiya, hukumomi masu kula da lafiyar jama’a, da kwararru daga jami’o’i da sauran abokan hulda.

Dr. Hauwa Ibrahim, kwararriya a fannin jini, za ta kasance a matsayin sakatariyar kwamitin.

Sanarwar ta kara da cewa an bai wa kwamitin damar kara wasu masu ruwa da tsaki idan bukatar hakan ta taso, domin tabbatar da cikar burin inganta jinin da ake amfani da shi a Jihar Kano.





Source link

Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *