Majalisar dokokin jihar kano ta ce gyaran dokar canja sunan Yusuf Maitama sule University zuwa Northwest za ta yi gyara ne a kan sunan makarantar kawai ban da kunshin dokokin dake gudanar da ita.
Shugaban Masu rinjaye na majalisar Lawan Hussaini Dala ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan kudirin ya tsallake karatu na biyu.
Lawan Hussaini Dala ya jaddada cewa mayar da sunan jami’ar ainihin sunanta zai taimaka wajen cimma dalilin kafa ta.
A zaman na ranar Litinin, majalisar ta amince da karatu na biyu kan kudurin gyaran dokar malaman jami’o’i da kwalejojin jihar nan domin mayar da shekarun ritayar su daga aiki ya zuwa 70.
A cewar Dala gyaran dokar zai dace da tsarin dokar kasa da kuma cin gajiyar ilimin malaman a daidai lokacin da ya dace
Yayin zaman majalisar, ta ce za ta tabbatar da yin duk mai yiwuwa domin ciyar da fannin ilimin jihar Kano gaba.