Makiyaya sun nemi daukin gwamnati a Kano


Fulani makiyaya a karamar hukumar Doguwa ta jihar Kano sun roki gwamnatin jiha da ta tallafa musu da abincin dabbobi domin su samu damar kara samar da madara a yankin.

Shugaban makiyayan yankin (Ardo), Ahmadu Sulaiman, ya yi wannan roko ne yayin tattaunawa da ‘yan jarida a kasuwar shanu ta Falgore a ranar Jumma’a.

Sulaiman ya ce fiye da shanu 5,000 suna yawo a yankin karkashinsa, amma suna fama da rashin abincin dabbobi, ciki har da abinci mai gina jiki wanda zai sa su yi kiba.

“A halin da ake ciki, sama da shanu 5,000 na mu ba sa samun wadataccen abinci, domin damina ta kare, saboda haka muna bukatar gwamnatin jiha ta tallafa mana da abinci mai gina jiki wanda zai sa su yi kiba da kuma inganta samar da madara da nama,” in ji shi.

Ya kara da cewa, shanun da ke yankin suna samar da dubban lita na madara a kullum, wanda ake kaiwa kamfanonin sarrafa madara don yin yogurt da sauran kayayyakin madara.

Shugaban makiyayan ya kuma gode wa gwamnatin jihar bisa samar da asibitin dabbobi a kasuwar shanu ta Falgore ta hanyar aikin Kano State Agro-Pastoral Development Project (KSADP), wanda ya inganta lafiyar dabbobinsu.

Ya kuma yaba wa gwamnati bisa tabbatar da yin allurar rigakafin dabbobinsu akai-akai domin guje wa yaduwar cututtukan da ke haddasa mace-macen dabbobi.





Source link

Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *