NNPCL ya gayyaci Obasanjo ya ziyaraci matatar mai ta Fatakwal


Kamfanin Man Fetur na kasa (NNPCL) ya gayyaci tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya kai ziyara zuwa matatar man fetur ta Fatakwal da ke jihar Ribas.

A wata sanarwa da kamfanin ya fitar ranar Alhamis, NNPCL ya ce gayyatar na da nufin bai wa Obasanjo damar tantance matsayin aikin matatar wadda ta sake fara aiki kwanan nan.

Tsohon shugaban kasar, a wata hira da talabijin din Channels ya bayyana shakku kan cigaba da aikin matatar Fatakwal. Sai dai NNPCL ta ce ta cimma muhimman nasarori, kuma ta bukaci Obasanjo ya ziyarci matatar domin ya gani da kansa.

“Muna mika gayyata ga tsohon shugaban kasa mai girma don ya kasance tare da mu a wannan muhimmin tafiya. Hikimarsa da kwarewarsa na da matukar muhimmanci, kuma muna matukar godiya da shawarwarinsa da jagorancinsa,” in ji sanarwar NNPCL.

Kamfanin ya kara da cewa: “Muna gayyatar Shugaba Obasanjo zuwa ziyartar matatun da aka gyara don ganin ci gaban da aka samu. Muna matukar godiya ga gudummawar da ya bayar wajen ci gaban Najeriya.”





Source link

Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *