PDP za tai zawarcin Kwankwaso ya koma jam’iyyar


Jam’iyyar PDP ta bayyana aniyarta na neman Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon Gwamnan Kano kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, ya sake komawa cikinta.

Muƙaddashin Shugaban PDP na Ƙasa, Ambasada Umar Iliya Damagun, ya ce wannan yunƙuri na da nufin haɗa kai da Kwankwaso domin sake farfaɗo da jam’iyyar tare da ƙwatar mulki daga hannun Jam’iyyar APC a zaɓen 2027.

Damagun ya bayyana haka ne bayan da Kwankwaso, a wata hira da ya yi da BBC, ya caccaki PDP, inda ya bayyana cewa babbar jam’iyyar adawar ba za ta iya samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa ba saboda ta riga ta mutu.

Ya ce, “Nan ba da jimawa ba za mu tuntuɓi Kwankwaso domin har yanzu muna da yakinin cewa zai iya komawa PDP. Za mu haɗa kai da shi domin mu sake gina jam’iyyar tare da tunkarar wannan azzalumar gwamnati.”

Wannan furuci na Damagun ya zo ne kwana guda bayan Kwankwaso ya zargi tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, da yin ƙarya kan batun yarjejeniyar karɓa-karɓar mulki tsakaninsa da Peter Obi na jam’iyyar LP.

Haka kuma, Damagun ya amince da zargin Kwankwaso cewa cin fuskar da aka yi masa da sauran mambobin sa a PDP ne ya sa suka sauya sheƙa. Ya ce ya yi duk mai yiwuwa don hana ficewar Kwankwaso amma hakan ya ci tura.

Duk da haka, ya ce PDP a shirye take ta sake rungumar Kwankwaso da sauran tsoffin mambobinta da suka bar jam’iyyar saboda matsalolin baya.

“Ba mu daina fatan cewa Kwankwaso zai dawo ba. PDP ita ce tushen siyasarsa, kuma ita ta taimaka masa har ya kai matsayin da yake a yanzu. A shirye muke mu haɗa kai da shi domin mu sake karfafa jam’iyyar da fuskantar manyan ƙalubale nan gaba,” in ji Damagun.





Source link

Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *