A farkon safiyar Laraba, Rasha ta kai hari ta jirgin sama mai sarrafa kansa (drone) kan birnin Kyiv, babban birnin Ukraine, wanda ya jikkatar da akalla mutane uku tare da lalata gine-gine a unguwanni biyu.
Hukumar birnin ta bayyana cewa fashe-fashe sun mamaye sararin samaniya da safe bayan rundunar sojin sama ta Ukraine ta gargadi mutane kan zuwan jiragen sama masu sarrafa kansu zuwa birnin.
A cewar magajin garin Kyiv, Vitali Klitschko, “An dakile harin makiya ta hanyar kariyar sama, amma an lalata bangarori biyu na gidajen zama a yayin harin.”
Klitschko ya kara da cewa, “Tarwatsin ya kuma lalata wata muhalli da ba’ a zama a wani bangaren unguwar.”