Rundunar yan sandan jahar Kano, ta gurfanar da wasu mutane biyu , a gaban kotun majistire mai lamba 45, dake zaman ta a unguwar Gyadi-gyadi , karkashin jagorancin Mai Shari’a, Haulat Magaji.
An Gurfanar da Ado Yusuf da kuma Shehu Surajo, da Zargin hada kai don aikata da fashi da makami da kuma sumun kayan da aka Yi fashin a hannunsu.
Rahotanni sun ce tun a ranar 30 ga watan Nuwamban 2024, a garin Dambatta, Inda suka hada Kai wajen yi wa , Isma’il fashi ta hanyar yin amfani da sinadarin wata hoda sannan suka kwace masa babur dinsa mai kimar kudi N1,200,000.
Mai gabatar da kara, Barista Muhammed Sani, ya roki kotun ta bayar da dama a karanto musu kunshin tuhumar da ake yi mu su, inda kotun ta amince da rokon.
Bayan an karanta musu tuhumar nan ta ke suka musanta, Inda lauyansu ya nemi belinsu, sai dai kotun ta ce bata da damar bayar da belinsu, don haka ya nemi belinsu a gaban babbar kotun jahar Kano.
A bangaren lauyan Wadanda aka yi karar, ya yi suka kan tuhumar sakamakon rashin sanya wani sashi , sai dai lauyan masu karar ya ce Takaddar binciken farko ( FIR) da jami’an Yan Sanda suka gabatar ta isa komai domin akwai zargin fashi da makami a cikin ta.
Haka zalika ana zargin mutanen biyu, sun taba i wa wani matukin adaidaita sahu fashi , a unguwar Dandinshe, sannan suka gudu da Babur din.
Daya daga cikin lauyoyin masu karar , Barista Mustapha Yusuf Yakubu, ya ce mutanen da ake zargin sun addabi yankin Danbatta da sace-sace, fashi da kuma satar baburan adaidaita sahu.
Alkaliyar kotun Mai Shari’a, Haulat Magaji, ta dage ci gaban shari’ar zuwa ranar 14 ga watan Janairu 2025 don ci gaban shari’ar.