Sarki Sanusi II ya nada sabon hakimi


Mai martaba sarkin Kano, Muhammed Sunusi II, ya nada Alhaji Idris Adamu Dankabo a matsayin sarkin Gabas kuma Hakimin Kabo.

Mai martaba Sarkin ya ce ya an nada shi ne bisa cancanta da kuma irin taimakon da yake yi wa al’umma musamman marasa karfi da masu bukata ta musamman.

Khalifa Muhammad Sunusi II ya kuma yi kira a gare shi da ya yi koyi da irin halayen mahaifinsa, Jarman Kano, Alhaji Muhammad Dankabo.

Da yake nasa jawabin jim kadan bayan nada shi a matsayin Sarkin Gabas, Idris Adamu Dankabo ya godewa Allah, da kuma Mai martaba Sarkin Kano bisa ba shi wannan mukami tare da yin kira ga al’ummar karamar hukumar kabo dasu bashi hadin kai don sauke nauyin da aka dora masa na hidin tawa al’ummar karamar hukumar dama kano baki daya.

Al’umma da dama ne suka halarci fadar sarkin don shaida nadin.





Source link

Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *