Sarkin Kano na 15, Bayero ya dawo gida bayan ziyarar aiki zuwa Egypt


Masoya Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero da dama ne suka yarbe shi bayan dawowarsa daga kasar Egypt a yammacin Alhamis.

Masoya sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero sunyi cikar dango tareda cika tituna domin yin lale marhabun da dawowar Sarkin gida lafiya.

Idan dai za’a Iya tunawa Kimanin makonni biyu Kenan Alhaji Aminu Ado Bayero yabar Kano zuwa kasar Egypt domin ziyarar aiki.

A lokacin ziyarar ne ma Sarkin ya karbi bakuncin kungiyoyi daban daban na Yan Najeriya dake zaune a kasar ta Egypt.

Kazalika Sarkin ya gana da jami’ai na Gwamnatin Kasar da mambobin diflomasiya da daidaikun mutane wadanda suka tattauna akan harkokin kasuwanci da tattalin arziki da Kuma cigaban jihar Kano da Najeriya.

Bayan saukar sa a fadarsa dake Nassarawa Sarkin Kano. Na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero ya godewa dumbin al’umar da suka tareshi tareda yimusu addu’ar fatan alheri.





Source link

Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *