Sojoji sun cafke mutum 20 da ake zargi da kai hari Filato


Dakarun Operation Safe Haven (OPSH) sun kama mutane 20 da ake zargi da hannu a kisan da aka yi a al’ummar Tingbwa Gidan Ado da ke karamar hukumar Riyom ta Jihar Filato.

Manjo-Janar Abdulsalam Abubakar, Kwamandan OPSH, ne ya bayyana hakan a lokacin liyafar bikin Kirsimeti da aka shirya wa dakarun OPSH da runduna ta 3 ta Sojojin Najeriya a ranar Alhamis a Jos.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa a ranar 22 ga Disamba, ‘yan bindiga sun kai hari a al’ummar tare da kashe mutane 15.

Abdulsalam, wanda kuma shi ne Babban Kwamandan Runduna ta 3 (GOC), ya ce dakarunsu sun kuma gano tarin makamai da alburusai masu yawa.

“Bayan awanni na ci gaba da gudanar da ayyuka a cikin dare, mun kama mutane 20 da suka shiga kai tsaye ko kuma suka taimaka a harin da aka kai a kauyen Tingbwa Gidan Ado a karamar hukumar Riyom a ranar 22 ga Disamba.

“Mun kuma kwace makamai da alburusai masu yawa, wanda hakan ya dakile ‘yan ta’adda daga samun damar aiwatar da miyagun ayyukansu.

Kwamandan ya gode wa dakarun OPSH da Runduna ta 3 bisa sadaukarwar da suka yi don tabbatar da zaman lafiyar da ake morewa a halin yanzu a jihar.





Source link

Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *