Shugaban jam’iyyar APC mai mulki na kasa, Dr. Abdullahi Ganduje, ya bayyana cewa ‘yan Najeriya za su samu dalilin farin ciki a shekarar 2025.
A sakon sabuwar sahekara da ya fitar ranar Talata a Abuja ta hannun Mataimakinsa na musamman kan yada labarai, Oliver Okpala, tsohon gwamnan ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa za a samu walwala a shekarar mai zuwa.
A cewarsa, gyare-gyaren hangen nesa da Shugaban Kasa Bola Tinubu ya aiwatar sun fara samar da sakamako mai kyau wanda za a fi gani a fili a cikin sabuwar shekara.
Ya ce: “Bari in tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa, kafin Kirsimeti mai zuwa, tattalin arzikin ƙasar zai tsaya daram kuma ya inganta sosai.”
Ya shawarci yan kasa da su ribaci sabuwar shekara ta hanyar kaunar juna da hadin kai.