Tattalin arzikin kasa ya haɓaka da kashi 3.46 a rubu’i na uku na Shekarar 2024


Babban Bankin Kasa (CBN) ya sanar da cewa tattalin arzikin ƙasar ya samu ci gaba da kashi 3.46 cikin ɗari a rubu’i na uku na shekarar 2024, daga kashi 3.19 cikin ɗari da aka samu a rubu’i na biyu na shekarar.

CBN ya bayyana cewa haɓakar tattalin arzikin ya samo asali ne daga wasu ɓangarorin da ba na albarkatun man fetur ba, tare da nuna cewa bangarorin kamar noma, masana’antu, da fasahar zamani sun taka rawar gani wajen wannan cigaban.

CBN ya ce manufofin inganta kasuwanci da gwamnati da masu ruwa da tsaki suka aiwatar sun taimaka wajen samun wannan cigaban.





Source link

Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *