Yan Sandan Kano sun mayar da adaidaita sahun da aka sace ga mamallakan su


Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta mayar da baburan adaidaita sahun da aka sace guda biyu ga mamallakan su, bayan ta gano su a wata maboyar bata-gari da ke karamar hukumar Danbatta.

Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Jumu’a.

A cewar sa, an gano baburan ne a ranar 9 ga watan Disamba, sannan aka tabbatar da mamallakan su; Mamman Musa da Sani Isma’il, bayan sun gabatar da cikakkiyar shaidar mallaka.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa wadanda ake zargi da satar baburan, Ado Yusuf mai shekara 40 da Rabiu Suleiman mai shekara 35, sun rigaya sun gurfana a gaban kotu domin fuskantar hukunci daidai da laifin da suka aikata.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, CP Salman Dogo Garba, ya shawarci masu baburan Adaidaita Sahu da su rika kula da mutanen da suke dauka a baburansu domin kaucewa fadawa hannun bata-gari.





Source link

Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *