Za a kafa sabuwar Jami’ar tarayya a kudancin Kaduna


Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa jami’ar tarayya a Kudancin Kaduna.

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya sanar da hakan yayin ziyarar ta’aziyya ga iyalan Kukah a masarautar Ikulu, karamar hukumar Zangon Kataf a Jihar Kaduna a Litinin din nan

Shettima ya ce, “Tare da Sanata Katung da dan majalisar wakilai, mun tuntubi Shugaba Bola Ahmed Tinubu, kuma ya amince da kafa jami’ar tarayya a Kudancin Kaduna.”

Mataimakin Shugaban Kasar ya kuma bayyana shirin kafa Cibiyar Lafiya ta Tarayya (Federal Medical Centre) a Kafanchan, Jihar Kaduna.

A cewarsa, gwamnatin Shugaba Tinubu tana da kishin cigaban Kudancin Kaduna, inda ya bayar da misali da nadin Janar Christopher Musa a matsayin Babban Hafsan Tsaro na Kasa, wanda ke nuna jajircewar Shugaban Kasar wajen magance bukatun tsaro na yankin.

“Ku tabbata cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na tare da al’ummar Kaduna da kuma al’ummar Kudancin Kaduna a zuciyarsa,” in ji Shettima.





Source link

Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *